
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya jagoranci taron taya murnar cika shekaru 60 na tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, a Abuja. Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Ladi Kwali a otel din kasa da kasa na Abuja, ya samu halartar manyan baki daga sassan siyasar Najeriya.
Daga cikin wadanda suka halarta sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi. Bishop Matthew Kukah na cocin Katolikar Sokoto ya gabatar da jawabi mai taken “Shin dimokuraɗiyya na lalacewa ne a Afirka?” wanda ya ja hankalin mahalarta.
Atiku Abubakar ya jinjinawa Ihedioha, yana mai cewa yana da kyakkyawar dangantaka da shi, duk da bambancin ra’ayi a cikin siyasa. Ya bayyana cewa, “Akwai babbar dangantaka tsakanina da Emeka, kuma har gobe ina kallonsa a matsayin mutum mai amana.”
Taron ya kasance mai matukar tasiri, inda aka tattauna kan al’amuran siyasa da kuma matsalolin da ke fuskantar Najeriya a yau. An kammala bikin da liyafar cin abinci da aka gudanar a yammacin ranar Litinin.