Taron Ministocin ECOWAS a Abuja: Batutuwa 30 Zasu Tattauna

Ministocin ƙungiyar ci gaban tattalin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) sun fara taro a Abuja, inda zasu duba batutuwan da suka shafi yankin da kuma matsalolin da ƙasashen mambobi ke fuskanta a halin yanzu.

Zaman taron, wanda aka gudanar a hedikwatar ECOWAS, ya kasance a ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar. A cikin jawabin da ya yi na buɗe taron, Tuggar ya bayyana muhimmancin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsaro, ci gaban tattalin arziki, da kuma hadin kai a tsakanin kasashen mambobi.

Shugaban ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana cewa za a duba batutuwa 30 na musamman da suka shafi cinikayya, tsaro, noma, da zaman lafiya. Ya jaddada cewa taron yana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci, saboda akwai kalubale da dama da yankin ke fuskanta.

Haka zalika, taron na zuwa ne a lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gana da shugaban hukumar ECOWAS da shugaban Jamus, Walter Frank Steinmeier. Wannan ganawa ta jaddada ƙoƙarin Najeriya na dawo da hadin kai da kasashen da suka fice daga ECOWAS, musamman Nijar, Mali, da Burkina Faso.

Touray ya yi kira ga kasashen mambobi da su ƙara bada gudunmawa wajen cika kuɗaɗen da aka tsara don gudanar da ayyukan kungiyar, wanda ya ragu da kashi 40% a cikin shekaru shida da suka gabata. Ya bayyana cewa akwai bukatar dukkan kasashe su hada kai domin inganta zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin.

Taron ECOWAS a Abuja na da nufin tabbatar da cewa ana gudanar da harkokin siyasa da na tattalin arziki cikin lumana da hadin kai, tare da magance dukkan kalubalen da ke fuskantar ƙasashen Afrika ta Yamma.