
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi tsokaci kan yawan ‘yan siyasa da ke sauya sheka daga jam’iyya guda zuwa wata, yana mai cewa hakan ba don amfanin al’umma ne, sai dai don cimma burin kansu. Wannan bayani ya fito ne yayin da ya ke magana da manema labarai a Kaduna, bayan taron kwamitin zartarwa na PDP na yankin Arewa maso Yamma.
Tambuwal ya bayyana cewa, “Sauya jam’iyya ba don buƙatar talakawa ake yi ba, sai don buƙatun ƙashin kai,” yana mai jaddada cewa wannan hali ya zama ruwan dare a cikin siyasar Najeriya. Ya caccaki gwamnatin APC, yana mai cewa babu tausayi da tsari a yadda ake gudanar da mulki a yanzu.
“Idan kai ɗan siyasa ne mai tausayi, ba za ka koma APC ba duba da halin matsin tattalin arziki da kuma gazawar gwamnatin Tinubu,” in ji Tambuwal. Ya kuma yi kira ga jam’iyyun adawa su haɗe kai domin fuskantar zabe mai zuwa a 2027, don samar da wata jam’iyya mai ƙarfi wacce ba APC ba.
Aminu Waziri Tambuwal ya ce, “Muna buƙatar haɗin kai don tabbatar da cewa a 2027 mun kawar da wannan gwamnatin da ta ci amanar ƴan Najeriya.” Wannan jaddawalin na Tambuwal ya nuna tsananin damuwarsa kan halin da siyasar Najeriya take ciki, musamman ma a tsakanin ‘yan siyasa da ke sabawa juna don amfaninsu.