
Talakawa sun yi tururuwa a gidan shugaban ƙasa Bola Tinubu a Bourdillon, Lagos, suna neman tallafi na Kirsimeti. Wannan al’amari ya jawo caccaka daga jam’iyyun hamayya, musamman PDP da LP, wadanda suka zargi gwamnatin APC da jefa ‘yan Najeriya cikin talauci da yunwa.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa wannan lamarin yana nuna irin wahalar da ‘yan ƙasa ke ciki a yanzu, yana mai cewa talaucin da ke akwai ya sa mutane suna dogaro da tallafi fiye da kima. Sakataren yada labaran jam’iyyar LP, Obiora Ifoh, ya zargi APC da jefa ƙasar cikin halin talauci, wanda hakan ya jawo dogayen layukan jama’a suna jiran tallafi.
Dan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa manufofin gwamnatin APC sun jefa Najeriya cikin mawuyacin hali, yana mai cewa hakan alama ce ta gazawa a shugabanci.
Jam’iyyar YPP ta kuma bayyana damuwa kan yadda tsare-tsaren tattalin arziki suka tsananta wahalar da ake ciki, suna kira da a sake duba su. Al’amuran suna ci gaba da jawo hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.