‘Ta Faru Ta Kare, Tinubu Ya Kori Ma’aikatan Gwamnati Masu ‘Digiri Dan Kwatano

Gwamnatin tarayya ta sallami ma’aikatan da suka yi karatu a wasu jami’o’in Jamhuriyar Benin da Togo daga shekarar 2017 zuwa yau. Wannan mataki ya biyo bayan shawarar da kwamitin da gwamnati ta kafa ya bayar domin tsaftace ma’aikatu daga masu takardun bogi.

Daraktan sadarwa na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya tabbatar da wannan mataki ga jaridar The Punch, yana mai cewa hukumar NYSC ta fara aiwatar da wannan umarni, inda aka kori ma’aikata biyar da aka dauka aiki da kwalin ‘digiri dan kwatano’.

Kwamitin binciken takardun digiri da gwamnati ta kafa ya gano cewa wasu daga cikin jami’o’in suna bayar da digiri alhalin matakin karatunsu bai cika ka’ida ba, wanda ya sa dole a kori ma’aikatan. An umarci ma’aikatu da hukumomi su gano ma’aikatan da aka dauka aiki da digiri dan kwatano daga 2017.

Wannan matakin na gwamnati yana da nufin tsaftace ma’aikatu daga matsalolin da suka shafi daukar aiki da takardun bogi. Daraktar NYSC, Caroline Embu, ta tabbatar cewa ma’aikata biyar ne aka sallama bisa bin umarnin ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya bayyana bukatar gano masu amfani da takardun bogi a cikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin a kore su, yana mai cewa wannan yana da matukar muhimmanci domin inganta tsarin daukar ma’aikata a Najeriya.