Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Sule Lamido Ya Koka Kan Mulkin APC a Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana damuwarsa game da mulkin jam’iyyar APC a Najeriya, inda ya kwatanta shi da mulkin Fir’auna. Lamido ya bayyana cewa, talauci da yunwa sun mamaye kasar, suna jefa al’umma cikin wahala.

A cikin wata hira da ya yi da gidan jaridar Tribune, Sule Lamido ya roki al’umma da su ba PDP dama a zaben 2027 domin gyara kura-kuranta. Ya yi nuni da cewa, jam’iyyun siyasa na yanzu suna neman mulki ne kacokan ba tare da ingantaccen tsari ba.

Lamido ya ce: “Muna bukatar ku ba mu lokaci, PDP za ta dawo da zaman lafiya da ci gaba.” Ya kara da cewa, al’ummar Najeriya na da rawar da za su taka wajen tabbatar da ingantaccen gwamnati.

Ya kuma kalubalanci gwamnatin APC, inda ya ce talauci ya zama makami a hannun shugabanni, yana mai jaddada cewa, al’umma ya kamata su tsaya tsayin daka wajen neman ‘yancinsu. Sule Lamido ya yi kira ga malaman addini su kasance jagorori a cikin al’umma, maimakon bin son zuciya a harkokin siyasa.

Lamido ya nuna cewa, duk da cewa gwamnati na ikirarin cewa komai yana tafiya daidai, al’ummar wasu jihohi kamar Zamfara, Kebbi, da Sokoto suna fuskantar matsaloli na tsaro da talauci.

A karshe, Sule Lamido ya ce, “Dole ne mu tashi tsaye domin kwato ‘yancinmu daga hannun mulkin da ba ya kawo ci gaba.”