
Kungiyar North-West Youths for Peace and Development (NWYPD) ta bayyana bukatar hadin kan al’umma wajen tallafawa sojojin Najeriya a kokarinsu na yaki da Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban kungiyar, Salihu Bello, ya bayyana cewa akwai bukatar al’umma su fahimci irin kokarin da sojojin ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A yayin ganawa da manema labarai a Abuja, Bello ya ce, “Sojoji na bukatar goyon bayanmu don dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma da sauran yankuna.” Ya kuma yi kira ga al’umma su daina goyon bayan duk wanda ke tallafawa ‘yan ta’adda, ko kai tsaye ko a boye.
Bello ya yaba wa kokarin da sojojin Najeriya ke yi a yaki da ta’addanci, yana mai cewa, “Dole ne mu yi nazari kan wadanda ke goyon bayan ‘yan ta’adda, saboda wannan ne zai taimaka wajen samun zaman lafiya a yankin.”
Haka zalika, ya yi jinjina ga shugabancin Janar Christopher Musa kan namijin kokarin da sojojin ke yi, tare da jaddada cewa al’umma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaro. Ya ce gwamnati na bukatar goyon bayan jama’a don samun nasara a wannan yaki.
Bayan haka, rundunar soji ta bayar da umarni ga al’umma da su kauce wa biyan kudade ga ‘yan bindiga, domin tabbatar da tsaron su. Wannan na zuwa ne bayan Bello Turji ya kakabawa wasu mazauna yankunan biyan Naira miliyan 25, wanda hakan ya jawo fargaba a tsakanin al’umma.