
A cikin wani mataki mai kyau na yaki da ta’addanci, dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan ta’adda 120 tare da cafke wasu miyagu 105 a makon da ya gabata. Wannan nasara ta kasance a tsakanin ranar 4 zuwa 10 ga watan Janairu, 2025, kamar yadda Manjo Janar Edward Buba, mai magana da yawun Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ), ya bayyana.
A cikin sanarwar da ya fitar, Manjo Janar Buba ya ce sojojin sun ceto mutane 43 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na kasar. Hakan na nuni da irin ƙoƙarin da sojojin ke yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas sun kashe ƴan ta’adda 64 ta hanyar hare-haren sama, yayin da dakarun Operation Fansan Yamma a Arewa maso Yamma suka hallaka 21 daga cikin ƴan ta’addan. Haka kuma, a Arewa ta Tsakiya, dakarun Operation Safe Haven sun kama miyagu 14 tare da ceto mutane 11.
Buba ya bayyana cewa sojojin sun kwato makamai da dama daga hannun ƴan ta’addan, ciki har da bindigogi da harsasai. Ya yi kira ga al’umma da su ba da haɗin kai ga sojoji domin kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Wannan nasara ta sojoji ta jaddada burin su na tabbatar da tsaro a duk fadin Najeriya, inda ake fatan ganin sun yi nasara nan bada jimawa ba