Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 74 a Mako guda

A cikin makon da ya gabata, sojojin Najeriya sun samu nasarori masu tarin yawa a yaki da ƴan ta’adda, inda suka hallaka ƴan bindiga 74 daga ranar 5 zuwa 13 ga watan Maris, 2025. Wannan bayani ya fito daga hedkwatar rundunar sojin Najeriya, wato DHQ, a cikin rahoton mako-mako na ayyukan tsaro.

Manjo Janar Markus Kangye, mai magana da yawun hedkwatar, ya bayyana cewa dakarun sojin sun kuma ceto mutane 61 daga hannun ƴan ta’adda a wannan lokaci. Har ila yau, ƴan ta’adda 143 sun miƙa wuya tare da ajiye makaman su a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A cikin wannan yaki, sojojin sun kwato makamai masu yawa, ciki har da bindigogi 71, wanda suka hada da bindigogi AK-47 guda 32 da kuma alburusai 1,202. Wannan nasara ta nuna karfin gwiwar dakarun tsaro a Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin ƙasar.

Manjo Kangye ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, tare da bin ka’idojin aiki da dokokin tsaro na kasa. Wannan nasara ta faru a lokacin da gwamnatin Najeriya ke ɗaukar matakai masu ƙarfi don yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro a fadin ƙasar.

Sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyukan su na yaki da ƴan ta’adda, suna fatan kawo karshen wannan matsala da ta addabi al’umma.