
Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka miyagun ƴan bindigar da ake zargi da kashe sojoji huɗu a jihar Ribas, Kudu maso Kudancin Najeriya. Rundunar sojin ta 6 da ke Fatakwal ta bayyana cewa an kashe ƴan ta’addan bayan sun yi yunkurin guduwa daga wurin da aka kai musu hari.
Kakakin rundunar, Laftanar Janar Danjuma, ya tabbatar da cewa dakarun sun yi artabu da ƴan bindigar a cikin wani samame a ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma. A yayin wannan samame, dakarun sojin sun hallaka ƴan bindiga guda biyu, wanda hakan ya kara tabbatar da kudurin su na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Danjuma ya bayyana cewa wannan ƙungiyar ƴan ta’addan ta kashe sojoji huɗu tare da yin garkuwa da injiniyoyi biyu daga Koriya, suna aiki tare da kamfanin Daewoo Nigeria Limited a ranar 12 ga Disamba, 2023.
A yayin samamen, sojojin sun kwato manyan makamai, ciki har da bindigogi samfurin AK-47 da wasu kayan aiki. Rundunar ta kuma nemi ƴan Najeriya da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka wajen kakkabe ƴan ta’adda a yankin.
Rundunar sojin Najeriya ta yi alkawarin ci gaba da yaki da dukkanin masu laifi da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a ƙasar.