Sojojin Najeriya Sun Hallaka Ƴan Bindiga 40 a Jihar Zamfara

Sojojin Najeriya sun cimma gagarumar nasara a jihar Zamfara, inda suka hallaka ƴan bindiga 40 a yayin da suka ƙwace iko daga hannunsu. Wannan lamarin ya faru ne bayan harin ramuwar gayya da ƴan bindigan suka kai, wanda ya biyo bayan kisan wani daga cikin shugabanninsu, Alhaji Sani Dan Garin Bawo.

Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma, tare da haɗin gwiwar Askawaran Zamfara, sun yi artabu da ƙungiyar ƴan bindigar a garin Mada, cikin ƙaramar hukumar Gusau. Masana kan harkokin tsaro sun bayyana cewa ƴan bindigan sun yi ƙoƙarin kai wa garin hari ne a lokacin da suka tattaru a ƙauyen Manya.

Bayan samun rahoton shirin kai harin, sojojin sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru, inda suka fafata da ƴan bindigan tare da taimakon ƴan sa-kai. A yayin musayar wuta, wasu daga cikin ƴan bindigan sun kutsa cikin garin Mada, suna ci gaba da harbe-harbe kan fararen hula.

Wani ganau ya bayyana cewa faɗan ya ɗauki awanni da dama, amma daga ƙarshe, sojojin da ƴan sa-kai sun yi nasarar fatattakar ƴan bindigar. An kuma turo ƙarin dakaru cikin gaggawa don tabbatar da tsaron garin.

Bayan wannan fafatawa, sojojin sun ƙara ƙarfafa yawansu a Mada domin hana sake faruwar wani harin daga ƴan ta’adda. Hakan na nuni da cewa sojojin na ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin, musamman bayan kisan shugaban dabar ƴan bindigar, Alhaji Sani Dan Garin Bawo, wanda aka dauka a matsayin gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma tsaurara matakan tsaro a jihar Zamfara don kare rayukan al’umma daga hare-haren ƴan bindiga.