
Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da ‘yan bindiga a jihar Imo, inda aka rasa rayukan jami’an sojoji guda biyu, yayin da wani kuma ya ɓace. Wannan arangama ta faru ne a ƙauyen Osina, a lokacin da sojojin suka amsa kiran gaggawa dangane da harin da ƴan bindigan ke kaiwa.
Joseph Akubo, kakakin rundunar sojin ta 34 Artillery Brigade, ya tabbatar da faruwar wannan lamari a cikin wata sanarwa. Ya bayyana cewa, bayan arangamar, sojojin sun bi bayan ‘yan bindigan, inda suka hallaka ɗaya daga cikinsu tare da kwato makaman da aka yi amfani da su a harin.
Akubo ya ce: “Abin takaici, an kashe jami’an tsaro guda biyu a yayin fafatawar, sannan wani guda ɗaya ya ɓace. Ƴan bindigan sun ƙwace makamai da suka hada da bindiga ƙirar AK-47.”
A halin yanzu, sojojin sun yi ƙoƙarin gano inda sauran ‘yan bindigan suke, amma sun tsere cikin daji bayan arangamar. Wannan lamari na ƙara jaddada kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin, musamman daga ƴan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyar ESN (Eastern Security Network), wacce ta kasance reshe na masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB).
Ana fatan hukumomi za su ƙara ƙoƙari wajen magance wannan matsala ta tsaro da ke ci gaba da barazana ga rayukan mutane a yankin.