
Dakarun soji a jihar Kebbi sun yi artabu da ƴan ta’addan ƙungiyar Lakurawa, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma kwato makamai masu yawa. Wannan samamen ya gudana ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta’addan.
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartaswa ta jihar Kebbi, AbdulRahman Zagga, ya bayyana cewa sojojin sun hallaka mambobin ƙungiyar guda biyu a yankin Rubin Bisa da Fana, a cikin ƙaramar hukumar Dandi. Ya ce, “Mun samu nasarar kashe ƴan ta’addan bayan samun bayanai daga rahotannin leƙen asiri.”
Zagga ya bayyana cewa wasu daga cikin ƴan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka ƙwato makamai da dama daga hannunsu, ciki har da bindigogi na zamani da alburusai. Wannan samamen ya biyo bayan koke-koken shugaban ƙaramar hukumar Dandi, Dokta Mansur Kamba, kan ayyukan ta’addanci da ƴan Lakurawa ke yi a yankin.
Ƴan ta’addan Lakurawa sun dade suna addabar al’ummar yankin, suna satar mutane domin neman kuɗin fansa da kai hare-hare kan mazauna. Jami’an tsaro sun bayyana cewa suna ci gaba da bin sawun waɗanda suka tsere domin tabbatar da an kawar da barazanar da suke yi wa yankin.
Gwamnatin jihar Kebbi ta yabawa dakarun sojin bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya, tare da kira ga al’umma su ci gaba da bayar da gudummawa ta hanyar samar da bayanai masu amfani. Wannan yunkuri na gwamnatin yana nufin fatattakar ƴan ta’addan da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da suke fama da matsalar tsaro.