
Ƙungiyar Patriots for the Advancement of Peace and Social Development (PAPSD) ta yi zargin cewa masu kira da a ayyana dokar ta ɓaci a jihar Zamfara suna da wata manufa ɓoyayya ta siyasa.
A cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa na ƙungiyar, Dr. Sani Shinkafi, ya fitar a ranar Asabar a Abuja, PAPSD ta ce babu wani dalili da ya dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, tana mai cewa abubuwan da ke faruwa a jihar ba su kai matsayin da za a iya ɗaukar wannan matakin ba.
Shinkafi ya yi zargin cewa kiran dokar ta ɓaci wani yunƙuri ne na tayar da hankula da kuma hana zaman lafiya a jihar, yana mai cewa an shirya hakan ne domin jefa jihar cikin ruɗani da rikice-rikicen siyasa, da kuma hana gwamnati mai ci ta Gwamna Dauda Lawal ci gaba da ayyukanta na cigaban jihar.
Ya kuma yi Allah-wadai da waɗanda ke ɗaukar nauyin matasa don gudanar da zanga-zanga domin cimma wannan manufa, yana mai cewa babu kamanceceniya tsakanin halin da ake ciki a Zamfara da jihar Rivers, inda aka taɓa ayyana dokar ta ɓaci.
Shinkafi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan hafsoshin tsaro da su ɗauki mataki cikin gaggawa don dakile barazanar tsaro a Zamfara, tare da yaba wa ƙoƙarin jami’an tsaro da suka dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara musu kwarin gwiwa da samar da kayan aiki domin fatattakar maƙiyan zaman lafiya.