
An shiga cikin jimami a jihar Kogi bayan rasuwar Suleiman Omika Mohammed, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kogi ta Gabas. Marigayin ya rasu ne a gidansa da ke Lokoja, babban birnin jihar, yana da shekara 45.
Rahotanni sun bayyana cewa, Suleiman Omika, wanda ya maye gurbin Nasir Agbodu a matsayin shugaban jam’iyyar ‘yan watanni da suka gabata, ya rasu cikin yanayi na ban al’ajabi. Lokacin da ya fara neman agaji, ya faɗi gaban gidansa, inda hakan ya jawo hankalin mutane.
Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Joel Salifu, ya bayyana wannan rasuwa a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APC, tare da yi wa iyalan marigayin ta’aziyya. Ya bayyana Suleiman Omika a matsayin mutum mai halin kirki wanda ya yi wa jam’iyyar hidima da gaskiya.
Rasuwar marigayin ta jawo babban bakin ciki a tsakanin mambobin jam’iyyar, yayin da suke fatan Allah ya gafarta masa, ya kuma ba da hakuri ga iyalansa. Suleiman Omika ya bar mata ɗaya da yara shida bayan rasuwarsa.