
A ranar Alhamis, 6 ga watan Maris, 2025, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Rabaran Daniel Okoh, ya halarci taron buda-baki tare da Musulmai a masallacin Al-Habibiyya da ke Abuja. Taron ya yi nuni da bukatar zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai biyu, musamman a wannan lokacin na Ramadan.
Rabaran Okoh ya jinjina wa kungiyar ‘Al-Habibiyya Islamic Society’ bisa shirin da suka yi na ciyar da masu azumi 2,300. Ya bayyana cewa irin wannan yunƙuri yana karfafa fahimta da jituwa tsakanin al’ummomi. Ya ce, “Musulmi da Kirista daya muke, dole ne mu nemi hanyoyin hadin kai domin samun zaman lafiya.”
Babban Limamin Al-Habibiyya, Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce shirin ciyarwa yana taimakawa mabukata ba tare da la’akari da addininsu ba, yana mai cewa ya kamata a inganta fahimtar juna a tsakanin al’ummomi.
Shugaban CAN ya shawarci al’ummar Najeriya da su fahimci addinai da juna domin samun zaman lafiya da mutunta juna. Ya jaddada cewa, “Muna da bambance-bambance, amma ainihi daya muke, ya kamata mu nemi hanyar hadin kai.”
Taron ya samu halartar malamai daga bangarorin addinai daban-daban, wanda ya bayyana sha’awar inganta zaman lafiya da hadin kai a Najeriya. Wannan taro na buda-baki ya zama wani muhimmin mataki wajen inganta zaman lafiya a lokacin da ake fuskantar rigima kan rufe makarantu a wasu yankuna na arewacin Najeriya.