Shugaba Tinubu Ya Fadi Amfanin da Cire Tallafin Man Fetur Ya Yi Wa Najeriya


Lahadi, Disamba 01, 2024 Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar cire tallafin man fetur, yana mai jaddada cewa wannan mataki ya zama wajibi domin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya. A jawabinsa a wajen taron yaye ɗalibai karo na 34 da 35 na jami’ar Fasaha ta tarayya dake Akure, Tinubu ya yi tsokaci kan yadda cire tallafin zai taimaka wajen inganta yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ba ya nufin azabtar da ƴan Najeriya, amma yana da nufin ceto ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki. Ya ce:

“Idan ba a cire tallafin ba, tattalin arzikin Najeriya zai durƙushe. Wannan mataki na cire tallafi yana nufin ceto al’umma daga halin rashin tabbas da aka tsinci kanta.”

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa cire tallafin man fetur yana haifar da sakamako mai kyau ga ƙasar, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa tana da masaniya game da wahalhalun da jama’a ke fuskanta. Ya yi bayanin cewa:

Cire tallafin na da matukar amfani wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, wanda ke fuskantar matsaloli na rashin inganci da kuma tsadar kayayyakin masarufi.
 
A cewar Tinubu, tallafin da aka yi a baya an yi shi ne tare da niyyar tallafawa talakawa, amma kyakkyawar rayuwar da muke tunanin muna yi ta kasance ƙarya ce. Wannan ya sa gwamnatin ta yanke shawarar daukar matakan da suka dace.


Shugaba Tinubu ya jaddada cewa duk da wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta, akwai fata da ci gaba a gaba. Ya na mai cewa:

“Matakan da muka ɗauka sun fara haifar da sakamakon da ake buƙata. Ina farin cikin sanar da ku cewa, tare da hadin kai da goyon bayan ku, za mu ga canji mai ma’ana a cikin ƙasar.”

Shugaba Tinubu ya yi kira ga ƴan Najeriya su fahimci cewa cire tallafin man fetur wani mataki ne da ya kamata a karɓa don ceto tattalin arzikin ƙasar. Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki kan inganta rayuwar talakawa da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa.