Shugaba Tinubu Ya Bayyana Sabon Tsarin Tattalin Arziki a 2025

A cikin saƙonsa na Sabuwar Shekara, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2025. Tinubu ya bayyana cewa hasashen tattalin arziki na wannan shekara na da kyau saboda nasarorin da aka samu a shekarar 2024.

Shugaban ya bayyana cewa kasuwar hannun jari ta samu ci gaba, wanda ya haifar da ribar biliyoyin Naira, tare da samun karin zuba jari daga ƙasashen waje. Wannan yana nuna cewa kasashen duniya sun fara amincewa da tattalin arzikin Najeriya.

A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi alkawarin rage hauhawar farashi daga kashi 34.6% zuwa 15% ta hanyar ƙara samar da abinci da inganta ƙera magunguna a cikin gida. Haka zalika, gwamnatin tarayya ta shirya kafa kamfanin ba da lamuni na ƙasa domin tallafawa talakawa, mata, da matasa.

Shugaban ya ƙara da cewa burin gwamnatin sa shi ne gina tattalin arzikin Najeriya ya kai darajar Dala tiriliyan ɗaya. Wannan yana nuni da cewa akwai shirin inganta hadin kai tsakanin matakan gwamnati domin tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Haka kuma, Tinubu ya sanar da niyyar ƙaddamar da kundin kasa mai suna ‘National Values Charter’ da zai inganta dabi’u masu kyau da amana tsakanin ‘yan ƙasa da gwamnati. Ya kuma nemi haɗin kan jama’a domin guje wa abubuwan da ke kawo rarrabuwar kawuna.

A karshe, Tinubu ya gode wa ‘yan Najeriya bisa hakurin da suka yi a cikin lokacin da ya gabata, yana mai tabbatar musu cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don inganta rayuwar al’umma a shekarar 2025.