
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana damuwarsa kan rikicin sarautar da ake fama da shi a jihar Kano tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II. Wannan jawabi ya fito ne a yayin tafsirin Ramadan da ya gudanar a Abuja.
Sheikh Pantami ya ce wannan rikici yana da matukar tayar da hankali, yana mai cewa ba a taba tunanin za a ga irin wannan yanayi a Kano ba. Ya yi kira ga al’umma da su rika hakuri tare da saka bukatun al’umma a gaba domin samun mafita mai dorewa.
Malamin ya bayyana cewa, “Kano jiha ce mai matukar muhimmanci ga Arewa, don haka akwai bukatar a magance rikicin.” Ya kuma roki Allah da ya kawo karshen wannan rikici, yana mai cewa yana da matukar muhimmanci a samu zaman lafiya a jihar.
Haka zalika, Pantami ya koka kan yadda tarbiyya da tattalin arziki suka tabarbare a Arewa. Ya ce, “A baya, akwai girmamawa ga manya da masu kananan ayyuka, amma yanzu matasa da dama sun rasa shugabanni masu shiryar da su.”
Malamin ya yi addu’ar cewa Allah ya kare Kano da sauran jihohin Arewa daga tashin hankali da rikicin sarautar da ke faruwa. Wannan jawabi na Pantami ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da zamantakewa a Kano, yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen zaman lafiya a yankin.