
An shiga cikin yanayi na jimami a Maiduguri, birnin jihar Borno, bayan rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin Musulunci, Farfesa Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar. Sanarwar rasuwar ta fito ne daga shafin Facebook na malamin, inda ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta rasu bayan fama da jinya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana’iza a ranar Asabar, 22 ga Maris, 2025, a babban masallacin 505 da ke Maiduguri, da misalin karfe 10:00 na safe. A cikin sanarwar, Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar ya bayyana cewa, “Innalilahi wa’inna ilahi raji’un. Mahaifiyata ta rasu, za a yi sallar jana’izarta yau.”
Majiyoyi sun ce an gudanar da jana’izarta kamar yadda aka tsara, tare da halartar mutane da dama daga cikin al’umma. Wannan lamari ya jawo hankalin mutane da dama wanda suka yi addu’a ga mamacin, suna rokon Allah ya gafarta mata.
Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar ya sanar da cewa za a dakatar da karatun tafsirin Kur’ani da yake gudanarwa a masallaci har sai ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025, domin girmama rashin mahaifiyarsa.
Wannan lamari na rasuwar mahaifiyar malamin ya jawo hankalin al’ummar Musulmi a fadin jihar Borno, inda suke tura sakon ta’aziyya ga Farfesa Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar a wannan lokaci mai wahala.