
Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana goyon bayansa ga matakin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya dauka na janye shirinsa na hawan Sallah. Malamin ya ce wannan mataki yana da mahimmanci don tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.
Sheikh Khalil ya bayyana cewa zaman lafiya ya fi komai muhimmanci, yana mai jaddada cewa babu mulki mai amfani idan babu kwanciyar hankali. Ya roki shugabanni su fifita zaman lafiya tare da tunawa da irin gudunmawar da marigayi Ado Bayero ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin mulkinsa.
A cikin faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Khalil Network, Sheikh Khalil ya yaba wa Aminu Ado kan wannan shawara, yana mai cewa ya nuna cancantarsa a shugabanci. Ya ƙara da cewa duk mulkin da babu zaman lafiya ba zai iya ci gaba ba, don haka yana roƙon Allah ya kawo zaman lafiya da wadata a tsakanin al’umma.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta haramta duk wani hawan Sallah a wannan shekara don tabbatar da doka da oda, saboda karuwar rashin jituwa a jihar.