Sheikh Gumi Ya Mayar da Martani Kan Maganganun El-Rufa’i

Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi martani mai zafi kan sauya shekar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zuwa jam’iyyar SDP. Gumi ya bayyana cewa El-Rufa’i ya yi maganganu marasa dadi a baya, kuma yanzu ya kamata ya fuskanci abin da ya aikata lokacin yana kan mulki.

A cikin wata hira da aka yi da Gumi, ya ce, “El-Rufa’i ya yi rushe-rushe da zaluntar mutane, amma yanzu da aka kwace mulki a hannunsa, sai ya dawo yana kuka.” Malamin ya bayyana cewa wannan canji daga mulki zuwa zama ɗan adawa yana zama darasi ga sauran shugabanni masu girman kai a Najeriya.

Gumi ya yi nuni da cewa a lokacin da El-Rufa’i ke kan mulki, bai kula da ra’ayoyin mutane ba, kuma yana fatan hakan zai zama wa’azi ga dukkan shugabannin da suke rike da karagar mulki. Ya ƙara da cewa, “Matsalar shugabanni da dama ita ce suna girman kai idan sun samu mulki, ko kuma idan mutum ya samu kudi sai ya yi girman kai.”

A halin yanzu, bayan sauya shekar El-Rufa’i zuwa jam’iyyar SDP, ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa a zaben 2027, duk da cewa bai bayyana niyyar takarar shugaban kasa ba. Ana sa ran zai mara wa wani dan takara baya domin cimma burinsa na yaki da APC.