Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Rashin Nasararsa a Zaben 2019

Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawan Kaduna, ya bayyana a ranar Lahadi cewa ya rasa kujerarsa a zaben 2019 saboda kalubalen da ya yi wa gwamna Nasir El-Rufai akan yunkurin daukar bashi na dala miliyan 340. A cikin hirar da ya yi da manema labarai a Abuja, Sani ya ce, “Na dage wajen fadin gaskiya ga masu mulki, duk da cewa hakan ya sa na rasa kujerata.”

Ya bayyana cewa, gwamna El-Rufai da ‘yan majalisar jiha sun ki amincewa da shawararsa, wanda hakan ya haifar da matsaloli a jihar Kaduna. Sani ya kara da cewa, “Bashin ya hana ci gaban jihar, ya bar ayyuka barkatai ba a kammala su ba, kuma ya sa Kaduna ta zama jiha ta biyu mafi bashi a Najeriya.”

Tsohon sanatan ya bayyana cewa yana alfahari da cewa ya tsaya kan gaskiya, duk da cewa hakan ya jawo masa fushin wasu ‘yan siyasa. “Ina jin dadin cewa, idan na mutu, babu wanda zai ce ni ne na sa hannu kan bashin da za a biya har shekaru 100,” inji Sani.

Sani ya jaddada goyon bayansa ga Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna tare da bayyana shirin sa na takara a zaben 2027. “Na tsaya da gwamna, na biya farashin hakan ta rasa kujerata, amma yau na ga an tabbatar da gaskiyata,” in ji shi.

A karshe, Sani ya ce dalilin da yasa yawancin ‘yan majalisa ba sa dawowa shine rashin biyayya ga gwamnoni a jihohinsu, wanda hakan yake zama musu barazana a siyasa.