Shehu Sani Ya Bayyana Aniyarsa Ta Sake Tsayawa Takara a 2027

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa yana shirin tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2027. A cikin wata hira da ya yi a ranar Lahadi, Sani ya bayyana cewa zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Gwamna Uba Sani ya sami damar komawa kan kujerarsa a wa’adi na biyu.

Shehu Sani ya bayyana cewa, “Duk wani ɗan siyasa da ke son tsayawa takara yana dogara ne ga yanayin siyasa wanda ya yi daidai da muƙamin da zai nema.” Ya ƙara da cewa, “Idan abubuwa suka zo daidai kuma lissafin siyasa ya tafi yadda ake so, zan tsaya takara musamman don kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya.”

A yayin da yake gabatar da saƙon bikin ƙaramar Sallah a gidansa da ke Kaduna, Sani ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, “Abin da yafi zama muhimmanci a gare mu shi ne tabbatar da cewa gwamna mai ci, Uba Sani, ya sami damar yin tazarce.” Sani ya tabbatar da cewa za su yi aiki tuƙuru domin cimma wannan burin.

Duk da ƙalubalen da za su fuskanta, Sani ya nuna karfin gwiwa cewa suna shirye don fuskantar duk wata matsala da ka iya tasowa. Haka zalika, ya yi Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta a jihar Edo, yana mai kira ga hukumomin tsaro su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

A ƙarshe, Shehu Sani ya jaddada cewa dukkan ƴan Najeriya su yi aiki tare don ganin ƙasar nan ta gyaru, tare da tabbatar da dimokuraɗiyya a cikin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *