SERAP Ta Shigar da Kara Kan Dakatar da Sanata Natasha a Kotun Tarayya

Kungiyar kare hakkin dan adam ta SERAP ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba bisa ka’ida ba.

SERAP ta bayyana cewa, dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha na tsawon wata shida ta tauye hakkin ta na wakilci a majalisar dattawa, wanda hakan ya shafi al’ummar Kogi ta Tsakiya. Kungiyar ta nemi kotu ta soke wannan dakatarwar, tana mai cewa ta sabawa kundin tsarin mulki na Najeriya.

A cikin sanarwar da SERAP ta fitar, mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya bayyana cewa, “Dakatarwar ta hana al’ummar Kogi ta Tsakiya samun wakilci a majalisar, wanda hakan ba zai iya zama daidai ba.”

Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha bisa zargin yin magana ba tare da izini ba da kuma ƙin amincewa da sabon wurin zama da aka bata. Wannan dakatarwar ta hana ta shiga harkokin majalisa da kuma samun albashinta da duk wani alawus da take da hakki a kansa.

SERAP ta yi watsi da wannan mataki, tana mai cewa, kasancewar sanata ba ya hana mutum samun hakkin bil’adama na asali da kundin tsarin mulki ya tanadar masa. Haka zalika, kungiyar ta jaddada cewa, majalisar dattawa ya kamata ta zama abin koyi wajen kare doka da hakkin dan adam.

A halin yanzu, SERAP na neman kotu ta hana majalisar dattawa sake dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan domin amfani da haƙƙinta na faɗin albarkacin baki. Koton ba ta sanya ranar sauraron ƙarar ba tukuna, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha ta gabatar.