Saurayin Da Ya Yi Kisan Kai Ya Yi Ikirarin cewa baiyi Nadama ba

Timileyin Ajayi, matashi mai shekaru 32, ya amsa laifin kashe budurwarsa, Salome Adaidu, wacce ke cikin shirin bautar ƙasa a Abuja. Wannan mummunan lamari ya faru a unguwar Papalana, New Karshi, jihar Nasarawa, inda Timileyin ya yanke wuyan Salome a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu.

Ajayi ya bayyana cewa bai yi nadama ba kan wannan kisa, yana mai cewa ya yi hakan ne sakamakon zargin cin amanar da Salome ta masa. Ya ce, “Na kashe ta ne saboda na gano tana hulɗa da wasu maza ta wayarta. Wannan ya fusata ni.”

Bayan faruwar wannan lamari, an kama Timileyin yayin da yake ƙoƙarin ɓoye sassan jikinta, kuma ‘yan sandan jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa za su gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce suna gudanar da bincike mai zurfi kan wannan lamarin, tare da tabbatar da cewa za a yi adalci ga iyalan marigayiyar. Iyalin Salome sun roƙi gwamnati da hukumomi su tabbatar da adalci da kuma hana irin wannan aika-aika a nan gaba.

Wannan lamari ya jawo hankalin al’umma kan matsalar kisan kai da ke addabar ƙasar, tare da kiran a dauki matakan gaggawa don magance wannan barazana ga zaman lafiya da tsaro.