Saurayi Ya Siyar wa Maryam Sa’idu Gidan N55m a Kano

An bayyana cewa wani saurayi ya siya wa fitacciyar ‘yar TikTok, Maryam Sa’idu, gida mai farashin Naira miliyan 55. Wannan mataki ya biyo bayan gajiyar da saurayin ya yi daga zaman Maryam a otel, inda ya yanke shawarar yi mata kyautar gidan don ta koma gida.

Maryam ta bayyana cewa gidan yana dauke da kayan da suka kai Naira miliyan 22. A cikin bidiyon da ta saki a shafukan sada zumunta, ta bayyana cewa ta yanke shawarar ba ta son yin aure a wannan lokaci, tana mai cewa:

“Waya ce maki aure ne na yi? Wallahi ba aure na yi ba. Saurayi na ya siya mani gida, ya ce ba ya son zamana a otel a Kano.”

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu amfani da intanet, inda wasu suka bayyana ra’ayoyin su kan wannan lamari. Wasu sun zargi Maryam da nuna cewa tana daukar matakan da ba su dace ba, suna mai cewa ta zama alama ta jarabawa da kudi.

Maryam ta dage cewa ba ta shirya yin aure yanzu ba, tana mai cewa:

“Auren me? Rufa mun asiri in yi aure yanzu, ai an daina yin haka.”

Bidiyon ya jawo hankalin mutane da dama, wasu suna caccakar Maryam bisa ga matakan da ta dauka, yayin da wasu suka yi ta jinjina wa saurayin bisa ga kyautar da ya yi mata. Wannan lamari ya bayyana yadda kudi ke shafar zamantakewar matasa a zamanin yau.