Sarki Sanusi II Ya Kauracewa Taimakon Gwamnatin Tinubu

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa ba zai tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen gyara kura-kuran da ta yi a tsare-tsarenta ba. Wannan furuci ya fito ne a lokacin taron cika shekaru 21 na Fawehinmiism da aka gudanar a Lagos.

A cewar Sarki Sanusi, duk da cewa yana da abokai a cikin gwamnatin, amma ba su nuna masa goyon baya da ya dace ba. Ya ce, “Ina da abubuwan da zan faɗa da suka saɓawa tsarinsu, amma na zaɓi na kama baki na daina yin magana.”

Sarkin ya bayyana cewa yana da abubuwan da zai iya bayar da shawara a kai, amma ya zaɓi kada ya yi hakan domin yana ganin hakan zai amfanar da gwamnati, wanda ba ya son taimaka musu. Sanusi ya ƙara da cewa gwamnatin ba ta da nagartattun mutane da za su yi wa mutane bayani mai kyau, wanda ya sa ya tsame hannunsa.

Sanusi II ya yi nuni da cewa halin da ake ciki yanzu ba sabon abu ba ne, saboda an riga an yi hasashen faruwar hakan tun shekaru da dama da suka gabata. Ya yi kira ga al’umma da su dage addu’o’in samun zaman lafiya da kariya daga fitintinu.

Wannan jawabi na Sarki Sanusi II ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, inda ya nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta duba cikin kanta don inganta tsarinta da gudanar da al’amura yadda ya kamata.