
A ranar Juma’a, 10 ga watan Janairu, 2025, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi magana mai karfi bayan hukuncin kotu da ya shafi rigimar sarauta a jihar Kano. A cikin jawabin nasa, Sanusi II ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa wannan hukunci, wanda ya ce ya zama babbar nasara ga masarautar Kano.
Sarkin ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da tsari, ya kuma yi addu’a ga masu neman fitina a Kano, yana mai cewa Allah ya jawo musu fitintinu a rayuwarsu.
“Sannan muna bukatar a ci gaba da tafiyar da lamura cikin kwanciyar hankali da biyayya da doka,” in ji Sarki Sanusi II. Ya kuma jaddada cewa wannan magana ta wuce mulkin dan Adam, yana mai cewa har yanzu suna fuskantar wannan fada da mulkin Allah.
Sarkin ya soki alkalin kotun da ya yanke hukunci, yana mai cewa sun san cewa ba su da hurumin yin hakan. Ya yi kira ga jama’a da su kiyaye zaman lafiya da adalci a tsakanin su.
Ya kammala jawabin nasa da fatan Allah ya kare rayukan mutanen jihar Kano daga tashin hankali, yana mai kira ga al’umma su ci gaba da addu’a don samun zaman lafiya a yankin.