
A jihar Osun, Sanata Olubiyi Fadeyi, wanda ke wakiltar Osun ta Tsakiya a majalisar dattawa, ya yi murabus daga jam’iyyar PDP. Wannan mataki na Fadeyi ya zo kwanaki kaɗan bayan Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam’iyyar.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Yuli, 2025, Sanata Fadeyi ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne sakamakon rikicin cikin gida da rashin jituwar da aka gaza gyarawa a cikin jam’iyyar. A cewarsa, “Rigingimu da rabuwar kai da har yanzu aka gaza warware wa tsawon shekaru a matakin ƙasa da yawan kai ƙara kotu ne ya sa na yanke shawarar fita daga PDP.”
Kodayake ya fice daga jam’iyyar, Fadeyi ya yi bayani cewa ya nemi shawarwari daga abokan siyasa da kuma iyalansa kafin yanke wannan hukunci. Wannan ficewar na Fadeyi shi ne na biyu a cikin awanni 24 a jihar Osun, bayan Sanata Francis Fadahunsi ya fice daga jam’iyyar PDP saboda rikice-rikicen shari’a da suka daɗe.
Wannan lamari na nuna cewa jam’iyyar PDP na fuskantar kalubale a jihar Osun, inda wasu daga cikin shugabanninta ke yanke shawara na fita daga jam’iyyar. Har yanzu, ba a bayyana inda Fadeyi da Fadahunsi za su koma ba.