Sanata Natasha Ta Karyata Rahotannin Neman Afuwa

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta karyata rahotannin da suka yi zargin cewa ta nemi afuwar Majalisar Dattawa kan dakatarwar da aka yi mata. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Sanatar ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin waɗannan rahotannin, inda ta ƙara da cewa har yanzu tana kan bakinta wajen kare haƙƙin mata.

Natasha ta ce, “Rahotannin da ke cewa na nemi afuwar majalisar dattawa ko kuma na janye matsaya ta ba gaskiya ba ne.” Ta bayyana cewa ba ta ba da wata afuwa ga majalisar ko wani ba, tana mai jaddada cewa burinta shine tabbatar da gaskiya da adalci.

Rahotannin sun bayyana cewa an dakatar da Sanata Natasha bayan wani sabani da aka yi tsakanin ta da shugabannin majalisar. Ta soki masu yada waɗannan labarai, tana mai cewa suna ƙoƙarin karkatar da gaskiya da yaudarar jama’a.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan jita-jita, tana mai cewa duk wata sanarwa daga gare ta za ta fito daga shafukanta na asali. Sanata Natasha ta bayyana damuwa kan yunƙurin da ake na hana ta yin magana a cikin majalisar, tana mai cewa wannan batu na shafar dimokuraɗiyya.

A yayin da take ci gaba da fafutukar kare haƙƙin mutanen da take wakilta, Sanata Natasha ta yi kira ga ƴan Najeriya su kasance masu lura da bayanai marasa inganci.