Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Gwamnan Jigawa

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, a ranar Juma’a. Ziyarar ta’aziyyar ta biyo bayan rasuwar mahaifiyar gwamnan, Hajiya Maryam, da ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi, wanda ya rasu a wani hatsarin mota.

Sanata Lawan ya bayyana cewa rashin ɗan uwa yana da matuƙar ciwo, musamman ma idan mutum ya rasa mahaifiya da ɗa a lokaci guda. Ya roki Allah ya ba gwamnan karfin gwiwa da juriyar wannan rashi mai raɗaɗi.

A lokacin ziyarar, Sanata Lawan ya bayyana cewa: “Rasuwar ‘yan uwa ba zato ba tsammani abu ne mai raɗaɗi, amma rashin uwa da ɗa a lokaci guda ya wuce duk yadda za a misalta.” Ya kuma bayyana cewa Hajiya Maryam ta kasance mai kishin addini da tallafawa mutane a cikin al’umma.

Daga cikin wadanda suka jajantawa gwamna Namadi akwai shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya aika sakon ta’aziyya ga gwamnan bisa wannan babban rashi. Ganduje ya ce rashin makusanta yana da ciwo, yana mai addu’ar Allah ya jikansu.

Ziyarar ta’aziyyar ta jawo hankalin al’umma, inda mutane da dama suka bayyana alhininsu bisa wannan rashin da ya faru ga gwamna Namadi da iyalansa.