
بسم الله الرحمن الرحيم
Bismillah al-Rahman al-Rahim
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
A farko dai Muslimi ya sani cewa Babu wata tabbataciyar Sallah na Neman Biyan bukata, a Koda yaushe Muslimi zai iya yin sallar Nafila a lokutan da suka dace musanman cikin dare Yana Mai rokan Allahu SWT duk Wasu bukatun sa
Anaso Muslimi ya gode ma Allah matukar gode wa tare da Neman gafarar sa
Anaso Muslimi ya kasance cikin
Alwuduh: A kasance cikin tsarki da Alwala Domin Kara kyautata tsakaninka da Ubangijin ka
Nafila: yayi Nafila mafi karanci Raka’a biyu, Mai Neman Biyan Bukata Yana iyan yin rakao’i fiye da biyu, a Yayin da Yazo sujuda sai yayi ta anbaton dukan bukatun sa
Tawwassul: An ruwaito cewa was Salihan bayi a lokacin da suka shiga wata matsala Mai Girma, sun kasance sunyi tawwasuli da ayyukar su na gari, suna masu rokon Allah da ita
Mai Neman Biyan bukata zai iya yin Tawwasuli da Ayyukan sa na gari Domin samun Biyan Bukatun sa
Hikimomin wannan Nafilar:
Neman Taimako daga Allah: tana koya wa Musulmi yadda za su je ga Allah a duk lokacin Neman Biyan bukata.
Samun Jin Ƙarfi da Natsuwa: A Lokacin da bawa yake Nafila dayin Addu’ar Allahu SWT Yana kawo masa kwanciyar hankali, yana rage masa damuwa sa. Wannan yana taimaka wa bawa ya ji cewa Allah yana tare da shi.
Zamantakewa da Tawhid: Dogaro ga Allah kan Biyan bukata tana tabbatar da imani da Tawhidi, wanda ke nufin cewa Allah ne kadai mai iko da dukan al’amura.
Kammalawa
A duk halin da bawa ya shiga, to ana so ya kusanci ubangiji Allahu SWT, kada ace bawo Yana cikin Jin dadi da Kwanciyar hankali, kada bawo ya kuskura a nisanci ubangiji Allahu SWT
Allah muke roko daya biya mana bukatun mu Ya gafarta mana zunuban mu