
A wani lamari mai tayar da hankali, fitaccen jarumin fina-finan Bollywood, Saif Ali Khan, ya fuskanci harin da wani dan ta’adda ya kai masa a gidansa a Mumbai. A ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, an ji cewa dan ta’addan ya shigo gidan jarumin da tsakar dare, inda ya daba masa wuka, wanda hakan ya haifar da jinya mai tsanani.
Bayan harin, an garzaya da Saif Ali Khan asibiti, inda aka yi masa tiyata don cire wukar da aka daba masa da kuma gyara raunukan da ya samu. Likitoci sun tabbatar da cewa jarumin yana cikin koshin lafiya bayan an kammala aikin tiyatar, kuma yana samun kulawa ta musamman daga likitoci.
Harin ya jefa iyalan Saif Ali Khan, ciki har da matarsa, jarumar Bollywood Kareena Kapoor Khan, cikin tsananin firgici. Duk da haka, ba a fitar da sanarwa daga garesu kan lamarin ba tukuna.
Rundunar ‘yan sandan Mumbai ta fara gudanar da bincike kan wannan hari, inda suka kafa kwamitoci don gano wanda ya kai harin. Kwamishinan ‘yan sandan, Dixit Gedam, ya bayyana cewa babu karin bayani akan wanda ya kai farmakin, amma suna ci gaba da bincike.
Kamar yadda aka sani, Saif Ali Khan ya shahara a fannin fina-finan Bollywood tun daga shekarar 1993, tare da fitowa a cikin fina-finai masu yawa, ciki har da Dil Chahta Hai da Kal Ho Naa Ho. Wannan lamari na harin ya jawo hankalin duniya, tare da fatan samun saurin waraka ga jarumin.