Sagagi Ya Karyata Zargin Jin Zugar Gwamna Abba Kabir

Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi, ya yi magana mai karfi kan batun zargin da ake yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jin zuga. A cikin wani bidiyo da ya wallafa, Sagagi ya bayyana cewa duk radadin da ake yi akan gwamnan ba su da tushe, yana mai cewa Abba Kabir mutum ne mai kyakkyawar niyya.

Sagagi ya bayyana cewa, lokacin da ya yi aiki tare da Abba Kabir, ya ga yadda gwamnan ke jajircewa a aikinsa, yana mai cewa yana da sabuwar manufa da ke kawo ci gaba ga jihar. Ya ce, “Abba Kabir mutum ne mai hakuri da kyakkyawar niyya, ba zai taba jin zuga ba.”

Har ila yau, Sagagi ya roki al’umma da su daina yanke hukunci kan gwamna ba tare da samun ingantaccen bayani ba, yana mai jaddada cewa wannan batu yana da matukar tasiri a kan zaman lafiyar jihar. Ya bayyana cewa yana godiya ga Abba Kabir akan damar da ya ba shi na rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamnati, duk da cewa an cire shi daga wannan mukami.

Sagagi ya kammala da fatan cewa gwamnatin Abba Kabir za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin nasara, tare da bayar da gudummawa ga cigaban jihar Kano.