
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana goyon bayansa ga kudirin kirkiro sabuwar jiha mai suna “Karaduwa” a jihar Katsina. Wannan kudiri zai cire wani bangare daga jihar Katsina domin samar da sabuwar jiha, wanda ke nufin kawo ci gaba a yankin.
Sanata Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a wajen taron rabon tallafi da aka gudanar a garin Funtua, inda ya jaddada cewa zai hada kai da Sanata Muntari Dan-Dutse wajen ganin an cimma burin kirkiro wannan jiha. Ya ce, “Zan yi aiki tare da Dan-Uwana, Sanata Muntari Dan-Dutse, domin tabbatar da samar da sabuwar jihar Karaduwa.”
A cewarsa, ƙirƙirar sabuwar jiha zai kawo ci gaba mai ma’ana ga al’ummar yankin, tare da haifar da karin damammakin tattalin arziki. “Karaduwa tana da cikakken arzikin noma da dukkan abubuwan da ake bukata don zama jiha. Ko da yake yana da wahala, amma yana iya yiwuwa,” in ji Jibrin.
Haka zalika, Sanata Muntari Dan-Dutse ya raba kayan tallafi ga mutanen mazaɓarsa domin taimaka musu a lokacin Ramadan, wanda ya hada da kayan abinci da kuma kayan sana’o’i. Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, wanda mataimakinsa ya wakilta, ya yi kira ga al’umma da su yi addu’a don ci gaban jihar da kasa baki daya.
Wannan kudiri na kirkiro jiha a Arewa na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar kalubale a fannin ci gaba da kuma inganta rayuwar al’umma. Jama’a na fatan cewa wannan sabuwar jiha za ta kawo canji mai kyau a cikin al’ummar Katsina da ma Arewa baki ɗaya.