Sabon Salon Garkuwa da Mutane ta Yanar Gizo Ya Kunno Kai

Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta gano wata sabuwar dabara ta garkuwa da mutane, inda masu laifi ke amfani da kafafen sada zumunta wajen yaudarar mata. Wannan sabon salon ya shafi mata 16 da aka ceto daga wannan hatsaniya tsakanin watan Satumban 2024 zuwa Janairun 2025.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Lagos, CP Olawale Ishola, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen suna amfani da dabaru na yaudarar mata ta hanyar yin soyayya da su a yanar gizo, suna kuma yi musu alkawura masu jan hankali. A lokacin da matan suka amince, ana tura musu tikitin jirgi da aka kashe har zuwa Naira 500,000, tare da kama musu masauki a manyan otal.

Bayan isowarsu Lagos, masu garkuwan na kwace wayoyinsu da duk wani abu da suka kawo, sannan su tura kudin zuwa asusun su. Daga nan, suna kira ga iyalan matan da aka yaudara, suna neman kuɗin fansa tare da yi musu barazana.

CP Ishola ya yi gargadi ga al’umma, musamman mata, da su kula da yadda suke hulɗa da mutane a kafafen sada zumunta, yana mai cewa duk wanda ya ga wani motsi da ba ya dace ya sanar da hukumomi.

Rundunar ta ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da cewa an dakile wannan sabon salon garkuwa da mutane, wanda ya zama babban kalubale ga tsaron al’umma.