Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Sabbin Jami’o’i 11 Sun Samu Amincewar Shugaba Tinubu

A ranar Litinin, 3 ga Maris, 2025, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin jami’o’i 11 a Najeriya domin inganta harkokin ilimi a kasar. Wannan mataki na gwamnati ya biyo bayan taron majalisar zartarwa (FEC) da aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja.

Ministan Ilimi na Tarayya, Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnatin tana daukar wannan mataki ne da nufin fadada damar samun ilimi a Najeriya. Ya ce sababbin jami’o’in za su fara aiki da lasisin wucin gadi, tare da jagorancin hukumomin da suka dace don tabbatar da cewa suna cika sharuɗɗan da aka gindaya.

A cewar Alausa, wannan yunkuri zai taimaka wajen rage cunkoso a jami’o’in gwamnati da kuma samar da karin guraben karatu ga matasa. Sababbin jami’o’in da aka amince da su sun hada da:

1. New City University, Ayetoro – Jihar Ogun
2. University of Fortune, Igbotako – Jihar Ondo
3. Eranova University, Mabushi – Abuja, FCT
4. Minaret University, Ikirun – Jihar Osun
5. Abubakar Toyin University, Oke-Agba – Jihar Kwara
6. Southern Atlantic University, Uyo – Jihar Akwa Ibom
7. Lens University, Ilemona – Jihar Kwara
8. Monarch University, Iyesi-Ota – Jihar Ogun
9. Tonnie Iredia University of Communication, Benin City – Jihar Edo
10. Isaac Balami University of Aeronautics and Management, Lagos – Jihar Lagos
11. Kevin Eze University, Mgbowo – Jihar Enugu

Wannan sabuwar kafa jami’o’in na da nufin inganta ilimi a Najeriya, wanda zai yi tasiri mai kyau ga matasa da kuma ci gaban kasa baki daya. Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ci gaba da karfafa duk wani yunkuri na habaka ilimi a fadin kasar.