
Mallam Nuhu Ribadu, mai ba da shawara kan tsaro ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya yi martani kan zargin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa yana shirin neman takarar shugaban kasa a shekarar 2031. Ribadu ya bayyana cewa ba zai yi gardama da El-Rufai ba, yana mai cewa yana da abubuwan da suka fi muhimmanci fiye da jayayya da shi.
A cikin martaninsa, Ribadu ya jaddada cewa bai taɓa sukar El-Rufai a bainar jama’a ba, saboda girmamawa ga dangantakarsu da iyalansu. Ya ce, “Ban taɓa tattaunawa da kowa kan takarar shugaban kasa a 2031 ba. Hankalina ya koma kan yadda za a inganta ci gaban Najeriya.”
Ribadu ya yi kira ga jama’a su yi watsi da kalaman El-Rufai a kansa, yana mai tabbatar da cewa duk hankalinsa na kan nasarar mulkin Tinubu da ci gaban ƙasar. Ya kuma roki El-Rufai da ya bar shi ya mai da hankali kan aikinsa, kamar yadda shi ma ba ya shiga harkokin El-Rufai.
Wannan martani ya biyo bayan zargin da El-Rufai ya yi cewa Ribadu na neman zama wani mai hannu a cikin harkokin siyasa a Arewacin Najeriya, domin guje wa duk wanda zai iya zama masa matsala. Ribadu ya bayyana cewa yana da abubuwan da suka fi muhimmanci da zai mai da hankali akai a halin yanzu.