
Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanar da rasuwar Kwamishinar Harkokin Mata, Mrs. Elizabeth Bidei, wanda hakan ya jefa al’umma cikin alhini. A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, gwamnan jihar, Douye Diri, ya nuna alhini kan wannan rashi, tare da jaddada cewa Mrs. Bidei ta kasance mamba mai muhimmanci a majalisar zartarwa.
Gwamnatin ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, musamman mijinta, Chief Jackson Bidei, da ‘ya’yansu. Sanarwar ta bayyana cewa za a ci gaba da tuna kyawawan ayyukan da ta yi wajen inganta rayuwar mata a jihar.
Mrs. Bidei ta kasance mai jajircewa wajen bunkasa hakkin mata, kuma gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a Yi matuƙar kewar ta saboda sadaukarwarta da aikinta. Gwamnati ta yi addu’a ga iyalan da suka rasa masoyiyarsu, tana mai fatan Allah ya ba su karfin hali a wannan mawuyacin lokaci.