
A cikin shekarar 2024, masana’antar Kannywood ta fuskanci rashi mai yawa tare da mutuwar fitattun ‘yan wasan kwaikwayo da mawaka. Wannan ya kasance babban abin bakin ciki ga masoya fina-finai da ma’aikatan Kannywood.
1. Rasuwar Saratu Gidado
A ranar 9 ga Afrilu, 2024, Saratu Gidado, tsohuwar tauraruwar Kannywood, ta rasu bayan ta kammala sahur. Tana da shekaru 56 a duniya, kuma rasuwarta ta yi matukar tasiri a cikin masana’antar. Manyan jarumai da shugabannin masana’antar sun bayyana kaduwa da wannan rashi, suna tuna gudunmawar da ta bayar a harkar fim tsawon shekaru 18.
2. Suleiman Alaka
A watan Yuli 2024, Suleiman Alaka, shahararren jarumi, ya rasu. Rasuwarsa ta kasance a ranar 22 ga Yuli, kuma darakta Al-Amin Ciroma ne ya tabbatar da wannan labari. Mutuwarsa ta kara dagula Kannywood, inda masoya fina-finai da abokai suka yi ta’aziyya ga iyalansa.
3. El-Mu’az Muhammad Birniwa
A ranar 5 ga Disamba, 2024, fitaccen mawakin Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa, ya rasu bayan ya kammala buga wasan kwallon kafa. Rasuwarsa ta janyo bakin ciki a cikin masana’antar, inda jaruman Kannywood da dama suka mika ta’aziyyarsu. El-Mu’az yana da matukar tasiri a fagen waka da fina-finai.
4. Baba Ahmadu
Bayan kwanaki kadan daga mutuwar El-Mu’az, Kannywood ta sake rasa Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da hedimasta wato babban Bashir a shirin “Dadin Kowa.” Rasuwarsa a ranar 16 ga Disamba, 2024, ta janyo babban alhini a cikin masana’antar. Shugaban hukumar tace fina-finai na Kano, Abba El Mustapha, ya yi addu’a ga Allah ya kai rahama ga jarumin.
Wannan jerin mutuwar fitattun ‘yan Kannywood a shekarar 2024 ya yi matukar tasiri ga masana’antar, inda al’umma ke fatan Allah ya Kara wa jarumman Nissan kwana da lafiya Mai dorewa