
Arewacin Najeriya na fuskantar manyan kalubale a fannin ilimi, inda yara miliyan 15 ba sa samun damar zuwa makaranta. Wannan rahoto ya bayyana cewa, matsalolin da suka fi shafar yara a wannan yanki sun hada da rashin tsaro, talauci, da al’adun gargajiya.
Mastalar tsaro
Rashin tsaro na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara zuwa makaranta, musamman a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa. Hare-haren Boko Haram sun tilasta rufe makarantu da dama, wanda hakan ya jawo hijirar dalibai da kuma lalata ginin makarantu. Rahoton Human Rights Watch ya nuna cewa, wannan matsalar ta jawo gwamnoni da dama sun rufe makarantu domin kare lafiyar dalibai.
Talauci A Arewa
Talauci yana daga cikin matsalolin da ke jawo rashin ilimi a Arewa, inda rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa sama da kashi 70% na al’ummar yankin suna rayuwa cikin talauci. Matsin tattalin arziki ya sa iyalai da dama sun fi bada fifiko ga abinci da kula da rayuwarsu fiye da tura yaransu makaranta.
Tasirin Al’adu
Al’adun gargajiya suna tasiri sosai wajen hana yara, musamman ‘ya’ya mata, zuwa makaranta. A wasu sassan Arewa, ana kallon auren wuri a matsayin wani muhimmin abu wanda ke hana ‘yan mata samun ilimi. Rahoton UNICEF ya nuna cewa hudu daga cikin mata goma a Najeriya ana aurar da su kafin su kai shekara sha takwas.
Duk da irin matsalolin da ake fuskanta, gwamnatin Najeriya tana kokarin magance wannan batu ta hanyar aiwatar da shirye-shirye kamar Safe Schools da NHGSFP, wanda ke bayar da abinci ga dalibai. Haka kuma, kungiyoyin duniya kamar UNICEF da gidauniyar Malala suna taimakawa wajen karfafa ilimi a yankin.
Dole ne a kara zuba jari da kokari wajen magance matsalolin ilimi a Arewacin Najeriya. Al’umma da kungiyoyi na da muhimmiyar rawa wajen inganta ilimi, wanda shine makullin kawo karshen talauci da bunkasa ci gaban al’umma. Ilimi na daga cikin muhimman abubuwan da za su kawo canji mai kyau ga makomar yara a wannan yanki.