Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Rarara Ya Yi Wankin Babban Bargo ga Shugaban Nijar Tchiani

Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya caccaki Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani, kan zarge-zargen da yake yi ga Najeriya. Rarara ya bayyana cewa zarge-zargen Tchiani suna cikin soki-burutsu, inda ya ce babu wanda ke cin dunduniyar Nijar kamar Tchiani.

A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa, Rarara ya ce: “Babban mai cin dunduniyar kasarsa shine Tchiani, wanda ya kwace mulki ya kuma rika ba da umarni a boye.” Hakan na zuwa ne bayan Tchiani ya zargi Najeriya da hada baki da Faransa don kawo cikas ga mulkinsa.

Rarara ya koka kan cin amanar da Tchiani ya yi wa tsohon shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, yana mai cewa al’umma na tsoron fadin gaskiya kan mulkin Tchiani. Ya kuma bayyana damuwarsa game da zarge-zargen da ke haifar da rikice-rikice tsakanin Najeriya da Nijar.

Bugu da ƙari, sarakunan gargajiya da mazauna kan iyaka a Sokoto da Kebbi sun musanta zargin Tchiani, suna mai cewa babu wani sansani na sojojin kasashen waje a yankunansu. Dagacin gundumar Balle, Alhaji Aminu Aliyu, ya karyata zarge-zargen, yana mai cewa maganganun Tchiani ba su da gaskiya.

Rarara ya yi kira ga Tchiani da ya daina zarge-zargen da ba su da tushe, domin inganta zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.