
Wasu gidajen mai a sassan Najeriya sun fara sayar da litar fetur a sabon farashi, bayan sanarwar matatar Dangote na rage farashin. Wannan ya biyo bayan ragin farashin da Dangote ya yi daga N970 zuwa N899.50 kan kowace lita, a matakin da aka dauka don rage wahalhalu ga ‘yan Najeriya.
Dillalan da suke sayo fetur daga matatar Dangote sun rage farashin da suke sayar da litar fetur da kashi 11.8%, daga N1,060 zuwa N939.50. Wannan sauyin farashi ya fara tasiri a gidajen mai a cikin awanni kaɗan bayan sanarwar Dangote.
Kamfanin MRS da wasu manyan dillalai suna sayar da litar fetur a farashin N939.50 a yanzu, wanda ya jawo farin ciki ga masu amfani da man fetur, musamman a wannan lokacin da ake bukukuwa.
Anthony Chiejina, jami’in Dangote Group, ya bayyana cewa wannan ragin farashi zai taimaka wajen saukaka tsadar sufuri, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara. Ya kuma yi kira ga masu sayen mai da su kiyaye wasu sharuda domin samun karin litoci.
Kungiyar manyan dillalan man fetur ta MEMAN ta sanar da cewa farashin shigo da litar fetur ya ragu zuwa N970 a watan Disambar 2024, idan aka kwatanta da N971 a Nuwambar 2024. Wannan ya nuna cewa akwai alamu na inganta harkokin man fetur a Najeriya.
Raguwar farashin man fetur na daga cikin matakan da gwamnati da masu ruwa da tsaki ke dauka don rage wahalar da al’umma ke fuskanta. Wannan sabon farashi na litar fetur yana nuni da cewa akwai kyakkyawan fata a fannin tattalin arziki da kuma kasuwancin mai a Najeriya.