
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa har yanzu babu wata yarjejeniya da jam’iyyar Labour Party (LP) ta cimma da wasu jam’iyyun siyasa kamar PDP da NNPP kan haɗaka a gabanin zaɓen 2027. Obi ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja.
Obi ya yi kira ga duk masu kishin kasa da su haɗa karfi domin ceto Najeriya daga halin da take ciki, yana mai zargin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta gaza wajen magance matsalolin tsaro da cin hanci. Ya bayyana cewa cin hanci ya ƙaru a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa akwai bukatar a haɗa kai don kayar da jam’iyyar APC.
Wannan magana ta Obi na zuwa ne kwanaki bayan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya tsakanin shi, Atiku Abubakar, da Obi kan haɗa kai. Obi ya nuna damuwa game da halin da Najeriya ke ciki, musamman matsalar tsaro da ta’addanci, yana mai cewa hakan na haifar da asarar rayuka.
Duk da haka, Obi ya yi fatan cewa masu kishin kasa za su fito su haɗa kai don kawo canji mai kyau a Najeriya a gabanin zaɓen 2027.