
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya zargi gwamnatocin Najeriya da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata, wanda ya haifar da tsananta talauci a ƙasar. Ya ce dole ne ‘yan Najeriya masu hannu da shuni su sadaukar da wani abu domin ceto al’umma daga fatara da rikice-rikice.
Obi ya bayyana cewa gwamnatoci sun bar aikin da ya rataya a wuyansu ga kungiyoyi da coci, yayin da jama’a ke cikin mawuyacin hali. Ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayar da gudummawar Naira miliyan 40 ga cocin Anglican na Diocese da jami’ar Godfrey Okoye University a Enugu.
Ya caccaki gwamnati a Najeriya, yana mai nuna bakin ciki cewa coci-coci da kungiyoyi masu zaman kansu suna gudanar da ayyukan da ya kamata gwamnati ta rika yi. Ya kuma yi kira da a karfafa ilimi a kasar nan, yana mai cewa al’umma tana samun ci gaba ne matukar ilimi ya samu tagomashi.