Peter Obi Na Iya Lashe Zaben 2027, Inji Nana Kazaure

Tsohuwar kakakin yakin neman zaben Obit-Datti a 2023, Nana Sani Kazaure, ta yi hasashen cewa Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, na da damar lashe zaben shugaban kasa na 2027 idan majalisa ta amince da dokar da za ta ba ‘yan takara damar tsayawa ba tare da shiga wata jam’iyya ba.

A cikin zantawarta da jaridar Punch, Kazaure ta bayyana cewa matasa suna karuwa wajen mara wa Obi baya, musamman saboda rashin jin daɗin mulkin Shugaba Bola Tinubu a halin yanzu. Ta ce, “Obi shine wanda matasa ke so, saboda sun fi jin zafin wannan gwamnatin fiye da ta baya.”

Nana Kazaure ta yi tsokaci kan yadda wannan sabon tsarin zai ba da damar mutum ya tsayawa takara ba tare da shiga wata jam’iyya ba. Ta bayyana cewa idan majalisa ta tabbatar da wannan kuduri kafin zaben 2027, Obi na iya amfani da wannan damar don cin zabe.

Ta ci gaba da cewa, “Idan har wannan dokar ta tabbata a Najeriya, to ina da tabbacin Peter Obi zai iya lashe zabe.” Wannan hasashen na Kazaure ya zo ne a lokacin da jam’iyyar Labour Party (LP) ke shirin tunkarar zaben 2027 da tsare-tsaren da za su kawar da Tinubu daga mulki.

A halin yanzu, jam’iyyar LP na gina tsarin jagoranci a jihohi 36 domin tunkarar zaben cikin ƙarfi da tsari, bayan kalubalen da ta fuskanta a zaben 2023. Wannan lamari na nuna cewa jam’iyyar na kan hanyarta ta dawo da karfin gwiwa da kuma kafa sabbin hanyoyi don samun nasara a zaben da ke tafe.