PDP Ta Kalubalanci Tinubu Kan Rashin Tsaro a Najeriya

Jam’iyyar PDP ta yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu tir da zarginsa na amfani da kididdiga marasa tushe wajen bayyana cigaban tattalin arzikin Najeriya. PDP ta ce tsare-tsaren gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta sun tsananta wahalar rayuwa ga ‘yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kakakin PDP na Kasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta soki maganganun Tinubu kan cewa ‘yan Najeriya suna iya yin tafiya lafiya ta hanyoyi. PDP ta bukaci Tinubu ya yi tafiya daga Abuja zuwa Legas domin ganin halin da talakawa ke ciki dangane da tsaro.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa, matsalolin rashin tsaro kamar garkuwa da mutane da fashi na ci gaba da addabar Najeriya, wanda hakan ya jawo mutuwar mutane sama da 80 a wasu jihohi. PDP ta yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta dauki matakan da suka dace domin inganta tsaro a cikin ƙasar.

Hakanan, PDP ta caccaki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur ba tare da tanadin matakan rage wahalar da talakawa ke ciki ba, wanda hakan ya haifar da tsadar rayuwa da durkusar da masana’antu.

PDP ta yi kira ga shugaban da ya duba halin da ake ciki tare da daukar matakai masu inganci don magance matsalolin tsaro da talauci a Najeriya.