PDP Ta ba Jonathan tikitin takara da Tinubu a 2027? Jam’iyya tayi bayani

Jam’iyyar PDP ta yi bayani kan rahotannin da ke cewa tana zawarcin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin ya yi takara a zaɓen 2027. Mataimakin daraktan yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Ibrahim Abdullahi, ya musanta wannan batu a wata tattaunawa da jaridar BBC Hausa.

Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa PDP ba ta ba Jonathan tikitin takara ba, kuma ba ta yi masa kiran yin takara a ƙarƙashinta. Ya jaddada cewa Jonathan ɗan jam’iyya ne, kuma PDP ta yi masa komai a lokacin mulkinsa.

Haka zalika, ya ce ko tattauna batun takarar Jonathan ba su yi ba, yana mai cewa “babu yadda za a yi su yi zawarcin Jonathan.” Ya kuma ƙara da cewa duk wanda ke son yin takara ƙarƙashin PDP yana da damar yin hakan.

Wannan musayar ta zo ne a lokacin da ake ta gabatar da wasu fastoci a Kano da ke goyon bayan Jonathan ya yi takara a zaɓen 2027, wanda hakan ya jawo cece-kuce a fagen siyasar Najeriya.