
A ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025, an samu labarin rasuwar Pascal Gabriel Dozie, fitaccen attajirin ɗan kasuwa kuma shugaban MTN na farko a Najeriya. An bayyana cewa ɗansa, Uzoma Dozie, ne ya fitar da sanarwar rasuwar mahaifinsa a madadin iyalansu.
Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani
1. Haihuwa: An haifi Pascal Dozie a ranar 9 ga Afrilu, 1939, a garin Egbu, jihar Imo.
2. Shekaru: Ya rasu yana da shekara 85, kwana ɗaya kafin ranar haihuwarsa ta 86.
3. Iyayen Sa: Ya taso a cikin gidan mabiya ɗarikar Katolika, inda mahaifinsa ya kasance malami.
4. Ilimi: Ya yi karatu a makarantun Our Lady’s School da Holy Ghost College a Owerri.
5. Digiri: Ya samu digiri a fannin Operational Research da Industrial Engineering daga Jami’ar City, London.
6. Gudummuwa: Ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban harkokin bankuna da sadarwa a Najeriya.
7. Diamond Bank: A shekarar 1990, ya kafa Diamond Bank, wanda ya haɗu da Access Bank a baya-bayan nan.
8. Jagoranci: Ya kasance shugaban MTN Nigeria, inda ya taimaka wajen sauya tsarin sadarwa a ƙasar.
9. Karramawa: An karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa, CON, bisa ga jagorancinsa.
10. Iyali: Ya bar mata ɗaya, Chinyere, da ‘ya’ya guda biyar.
11. Ta’aziyya: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Dozie, yana bayyana shi a matsayin gwarzon shugaba mai hangen nesa.
Rasuwar Pascal Dozie ta kasance babban rashi ga Najeriya, wanda ya bar tarihi mai haske a fannin kasuwanci da sadarwa.